An shiga rana ta karshe a taron G8

Taron kasashen G20 a Seoul
Image caption Yau ake shiga rana ta karshe a taron kasashen G8 dake gudana a Seoul, babban birnin kasar Korea ta Kudu

Shugabannin kasashen nan 20 masu karfin tattalin arziki, wato G-20 sun shiga rana ta karshe a taron da suke yi a Seuol babban birnin Korea ta Kudu.

Yayin taron dai an fuskanci takaddama dangane da batun nan na manufofin kasashen dangane da darajar kudadensu, inda wasu kasashe ke nuna damuwa game da yadda wasu kasashen ke rage darajar kudadensu da nufin karfafa fitar da kayan da suke kerawa zuwa kasawannin kasashen waje

Sai dai tabbas sanarwar karshen wannan taro zata yi kira ga wasu kasashe su daina dabi'ar nan ta rage darajar kudadensu da nufin jawo kasuwa ga kayan da suke kerawa.