Tarihin Yaya Toure

 Yaya Toure
Image caption Yaya Toure ne dan wasan da ya fi kowanne daukar albashi a gasar Premier ta Ingila

Bayan lashe lambobi da dama a 2009, a bana ne Yaya Toure ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin ‘yan wasan da suka kware a duniya.

Dan wasan wanda Barcelona ta sayar da shi ga Manchester City, ya zamo dan wasan da ya fi kowanne daukar albashi a tarihin gasar Premier, inda yake karbar fan 221,000 a kowanne mako.

Ya kuma zira kwallo a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Yana buga wasa kodayaushe a Manchester City, inda yanzu suke mataki na hudu – kuma ake damawa da su.

Duk da cewa Ivory Coast ba ta taka rawar gani ba a gasar cin kofin duniya a Afriak ta Kudu, Toure ya buga baki dayan wasannin da kasar ta buga.

Baya ga kwallon da ya zira a karawarsu da Koriya ta Arewa, ya kuma taimakawa Drogba a kwallon da ya zira a wasansu da Brazil.

Ra'ayin kwararru - da Steve Vickers

Babu shakka Yaya Toure ya cancanci zama zakaran dan kwallon Afrika na BBC – don haka yana bukatar kuri’arku.

Ya samu kyakkyawan yabo daga kociyan Manchester City Roberto Mancini, abinda yasa ya zamo dan wasa mafi daukar albashi a gasar Premier, inda yake karbar fan 221,000 a kowanne mako.

Duk da cewar Barcelona sun nuna ba sa son shi, amma babu wanda zai ce bai cancanci kudaden da yake dauka ba.

Ganin yadda yake taka leda, ga karfi, ga tsari – ya taimaka wa City zuwa mataki na hudu a gasar premier ta bana.

Duk da cewa Ivory Coast ba ta taka rawar gani ba a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu, Toure ya buga baki dayan wasannin da kasar ta buga.

Sannan ya zira kwallo daya sannan ya taimaka aka zira guda.

Ya kuma taka rawa sosai a wasan da suka lallasa Ghana da ci 3-1, a gasar cin kofin kasashen Afrika.

Ya kuma cancanci yabo ganin cewa Ivory Coast ta samu katin gargadi biyar ne kawai a gasar, amma babu Toure.

Akwai yiwuwar mu mayar da hankali kan ‘yan wasan gaba a wannan zaben, sai dai bai kamata mu manta da Yaya Toure ba.

Kuma duka a karshe, kudi sun nuna ko wanene shi!

Za ku iya zaban ne ta hanyar latsa wannan rariyar likau din da ke biye:

http://www.bbc.co.uk/worldservice/africa/2010/11/101111_afoy_2010_vote_page.shtml

Ko kuma ta lambar waya +44 7786200070