Mayakan Taliban sun kai hari a Afghanistan

Bam din da ya tashi a mota a Afghanistan
Image caption Bam din da ya tashi a mota a Afghanistan

Mayakan Taliban sun kai hari a filin jirgin sama da sansanin sojin da ke Jalalabad a gabashin kasar Afghanistan.

Dakarun kawance na kungiyar NATO sun ce akalla mayaka takwas ne suka rasu a ba-ta-kashin da aka kwashe sa'o'i biyu ana yi tsakanin ’yan Taliban din da sojin Afghanistan da ma na kungiyar kawancen.

Har ila yau, kungiyar ta NATO ta sanar da cewa an kashe dakarun ta uku a wani harin da aka kai a kudancin kasar.

To amma ba ta yi wani karin haske akai ba.

A lardin Kunduz da ke arewacin Afghanistan kuma mutane goma ne suka halaka lokacin da wani bam da aka dana a wani babur ya tashi a wata kasuwa da ke cike makil da jama'a.