Bincike ya gano makaman China a Darfur

Yankin Darfur na Sudan
Image caption An mikawa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wani rahoto daya nuna cewar ana shigar da makaman kasar China cikin yankin Darfur na Sudan

Bayan China tayi ta shafe makonni tana kawo jinkiri, daga karshe dai shugaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya karbi rahoton nan da ake ta cece-kuce akansa dangane da keta takunkumin majalisar dinkin duniya da ya haramta shigar da makamai yankin Darfur na kasar Sudan.

Rahoton wanda kwamitin wasu kwararru ya rubuta ya gano cewa, gwamnatin Sudan ta keta wannan takunkumi, kuma China ba ta yi abin a zo a gani ba wajen hana shigar da makaman da ta kera yankin na Darfur.

Shi dai wannan rahoto yace, a yankin na Darfur an samu kwanson albarusai da aka kera a China, amma rahoton bai dora laifin aukuwar hakan akan kasar ta China ba.