An gano albarkatun man fetur a Algeria

Kasar Algeria
Image caption Kamfanin hakar mai na Gazprom yace ya gano rijiyoyin mai da kuma iskar gas a karon farko a yankin arewacin Afirka

Kamfanin hakar mai na kasar Rasha, wato Gazprom yace, ya gano rijiyoyin mai da kuma iskar gas a kasar Algeria

Wannan shi ne karon farko da kamfanin ya samu irin wannan cigaba a yankin arewacin Afirka.

Kamfanin na Gazprom ya kuma ce, tuni ya samu nasarar haka wata rijiyar fitar da mai a yankin Berkine, dake kilomita dari biyar daga babban birnin kasar, wato Algiers.

An dai yi aikin gano wadannan rijiyoyin mai ne da hadin gwiwar kamfanin makamashi na gwamnatin kasar ta Algeria, wato Sonatrach.