Kawancen CFDR sun nemi a tuhumi Tandja Mamadou

A jamhuriyar Niger hadin gwiwar tsoffin jami'yyun adawa a karkashin inuwar CFDR sun yi kira ga majalisar mulkin sojan CSRD da ta tuhumi tsohon shugaban kasar Niger ta kuma gurfanar da shi a gaban wata kotu bisa zargin abinda suka kira cin amanar kasa'.

Wannan kira da kawancen na CFDR suka yi, ya biyo bayan hukuncin da kotun kawancen tattalin ARZIKIN AFRICA ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO ta yanke a wannan wata, inda kotun ke kira ga sojojin da ke mulki da su sallami Malam MAMADOU TANDJA.

Sai dai a bangaren hadin gwiwar tsoffin jami'iyyu masu iko a lokacin ikon Malam MAMADOU TANDJA wato AFDR, sun ce tsohon shugaban kasar ya yiwa kasarsa aiki ne kawai.