Ba za'a sami nasarar kauda 'yan AlQaida ba inji sojin Burtaniya

Sojin Burtaniya
Image caption Rundunar sojin Burtaniya ta bayyana cewar ba fa za'a iya kawar da kungiyar nan ta AlQa'ida ba.

Babban hafsan rundunonin sojan Birtaniya, Janar Sir David Richards yace, ba za'a iya samun nasarar kawar da kungiyar Al-Qaeda ba,

Janar David Richard ya kuma kara da cewa, dole ne Birtaniya ta cigaba da zaman cikin shirin fuskantar barazanar hari daga masu tsaurin ra'ayin Islama nan da shekaru talatin masu zuwa.

A wata hira da yayi da jaridar Daily Telegraph, Janar Richards ya kuma ce dole ne Birtaniya ta cigaba daukar matakan kare 'yan kasar, maimakon yin tunani samun nasarar kawo karshen masu tsaurin ra'ayin Islama

Inda a shekaru goma ko biyar da suka gabata ne babban hafsan sojan Birtaniyan ya furta cewa, ba za'a iya samun nasara akan kungiyar Al-Qaeda ba, to da ya sha suka sosai.