An samu rabuwar kai a gwamnatin Isra'ila

Matsugunan Yahudawa
Image caption Matsugunan Yahudawa

Rahotanni na nuna cewa kan gwamnatin Isra'ila ya rabu bisa sabon tayin da Amurka ta yi mata na cewa, ta dakatar da gine-ginen matsugunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna a gabar yammacin kogin Jordan, na wucin gadi.

Amurka na neman Isra'ila ta dakatar da gineginen ne na tsawon kwanaki 90, amma tayin bai kunshi gabashin birnin Qudus ba.

A nata bangare Washington za ta karfafa ikonta na kin amincewa da duk wata kasa a duniya dake adawa da manufofin Isra'ila a gabas ta tsakiya, tare da bata sabuwar kariya ta tsaro.

A martaninta kungiyar Fatah ta Palasdinawa ta bayyana rashin gamsuwarta.