Sojojin Nijeriya sun kama mutane arba'in

Rundunar sojin Nigeria ta ce, ta kama mutane fiye da 40 wadanda ake zargi da sace maaikatan mai a jihohin yankin Niger/Delta.

Kakakin sojojin Laftana Kanar Sagir Musa, ya ce tun bayan fara aikin dakaru na musamman a watan Satumba, wadanda aka dorawa alhakin yakar sace-sacen ma'aikatan mai da farfasa bututan mai a yankin na Niger/Delta, ta samu nasarar dawo da doka da oda a birnin Aba, inda nan ne cibiyar kasuwancin yankin.

Ya ce an mika mutane 95 da ake zargi, ga 'yan sanda da hukumar leken asirin ta Nigeria SSS, domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

A jiya asabar ne dai rundunar sojin Nigeria ta gargadi gungun masu tada kayar baya cewa, daga yanzu ba za ta lamuncewa kafa sansanonin masu tada kayar bayan ba.