'Yan bindiga sun kashe wani soja a Maiduguri

Rahotanni daga jihar Borno a arewacin Nijeriya sun ce wasu yan bindiga sun harbe wani soja har lahira a jihar.

Hakan ta sa rundinar 'yan sandan jihar bornon ta kai wani sumame inda ta kama kimanin mutane 47 a wasu unguwanni.

Jihar Borno dai na daga ciki jihohin Nijeriya dake fama da matsalar tsaro, inda ko a makon jiya ma sai da jami'an 'yan sandan suka kama wata mata da makamai a cikin buhu.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, Alhaji Muhammadu Jinjiri Abubakar shi ne ya tabbar da wannan labari.

Ya kara da cewa za su dauki dukkan matakan da suka dace domin samar da tsaro a jihar Borno yayin bukuwan babbar sallah.