Aung San Suu Kyi ta ce zata saurari bukatun 'yan Burma

Aung San Suu Kyi
Image caption Aung San Suu Kyi

A cikin hirar da tayi a karon farko tun bayan sako ta, jagorar yan adawa a kasar Burma Aung San Suu Kyi, ta shaidawa BBC cewa, tana da aniyar sauraren abinda alummar kasar Burma ke so da ita kafin ta dau mataki na gaba.

Ms Suu Kyi ta ce ba ta tsoron a sake kama ta, duk kuwa da ta san hakan ka iya faruwa. Da aka tambaye ta ko, tana ganin cewa sukar gwamnati da take yi ne ya sa aka yi mata daurin talala, sai ta ce:

ba na tunanin haka, domin ni a cikin rahama nake idan ka kwatanta ni da wadanda ke gidan yari.

Don haka ba ni da wata madogarar yin wani korafi.

Na yi adawa da daurin talalar da aka yi min ne saboda na yi imani da dokokin kasa, kuma a gani na ba su da hurumin tsare ni karkashin doka.