An hau Arfa cikin nasara

Hajjin bana
Image caption Hawan Arfa

Alhazan da suka je aikin haji na bana a kasar Sa'udiya sun nufi Musdalifa a halin yanzu, bayan kammala mafi girman rukunin aikin hajjin a yau, wato hawan Arfa.

Akwai sauran 'yan ayyuka da suka rage ma alhazan na bana su fiye da milyan ukku, kafin su kama hanyar komawa kasashensu.

Ayyukan sun hada da yin hadaya, wanda ya kunshi yanka dabba don ciyar da marasa hali, da yin askin kamala aiki, da jifar shedan da kuma dawafin dakin Ka’aba.

Mahajjatan bana sun bayyana yadda sake tsarin sufuri da aka yi ya taimaka wajen saukaka da gaggauta isa filin Arafat fiye da yadda aka saba a shekarun baya.