Manoma sun koka da rangwamen da ake bayarwa

Manoman auduga a nahiyar Afirka sun yi kira ga kasashen nahiyar turai da Amurka da su rage rangwamen da suke baiwa manomansu.

Wani rahoto da aka wallafa na bayyana cewa yunkurin da kasashe masu arziki ke yi na taimakawa kananan manoma da 'yan kasuwarsu ta hanyar rage farashin kayan amfanin gona, yana yiwa manoman auduga daga yammacin nahiyar Afirka matukar illa.

A duk shekara, kasashen nahiyar turai da Amurka kan baiwa manoman audugarsu rangwamen biliyoyin daloli.

Suna bayar da wannan rangwamen ne domin daidaita adadin abinda manoman zasu samu, domin gujewa shiga cikin wani yanayi.

Sai dai wannan sabon rahoton na bayyana cewa wannan rangwamen da ake baiwa manoman audugar domin su kara yawan abinda suke samarwa a duniya, na rage adadin da su manoman nahiyar Afirka ke samu.

Manoman nahiyar Afirkan daga kasashe kamar irinsu Chad da Mali, su ne ke noma auduga mafi rahusa a duk duniya, wanda kuma wannan matakin da manoman dake da arziki ke dauka na gallaza musu.

Kamar yanda rahoton ya bayyana, a shekara, rangwamen da kasashe masu arziki kan bayar na janyowa manoman da ke kasashen nahiyar Afirkan asarar kimanin dala miliyan dari da arba'in da wani abu, ko ma fiye da haka.