Basussuka sun dabaibaye Girka da Ireland.

tattalin arzikin kasar Girka
Image caption tattalin arzikin kasar Girka

Wasu sabbin alkaluma sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Girka na cikin mummunan hali, fiye da yadda aka yi zato tun da farko.

Kungiyar Tarayyar Turai tace gibin kasafin kudin kasar, ya kai kashi 15 cikin dari, kusan sama da kashi biyu cikin dari na yadda aka yi hasashe.

Har ila yau bashinda ake bin kasar ta Girka ya linka adadin da kungiyar tarayar turai ta amince da shi.

Yanzu masana kan tattalin arzukin kasa da kasa na birnin Athens na duba yadda kasar ta Girka zata daidaita lamuranta.