Ireland ta ce ba ta bukatar tallafi

Tattalin arzikin Ireland
Image caption Ireland da wasu kasashen Turai sun dade suna fama da matsala

Jamhuriyar Ireland ta nace cewa ba ta bukatar tallafi daga Tarayyar Turai, bayanda bayanai suka nuna cewa ana matsa mata lamba ta karfi tallafi daga Tarayyar. Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da "abokan arziki", amma ta musanta cewa ta nemi taimako daga Tarayyar Turai.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta Ireland za ta nemi Asusun daidaita al'amuran kudi na Tarayyar Turai, domin neman kusan Yuro biliyan 80.

Amma mahukunta a Ireland sun ce rahoton ba shi da tushe.

Ana saran ministocin kudi na tarayyar za su tattauna batun matsalar ta Ireland a taron da za su yi a birnin Brussel ranar Talata.

Sai dai editan BBC mai kula da nahiyar Turai Gavin Hewitt, ya ce tuni aka fara tattaunawa tsakanin shugaban Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso da kwamishinan tattalin arziki Olli Rehn, game da matsalar ta Ireland.