Gobara ta kashe akalla mutane 40 a Shanghai

Gini yana cin wuta
Image caption An samu cikas a kashe gobarar

Wata mummunar gobara a birnin Shanghai na kasar Sin ta kone wani dogon gini, inda ta hallaka akalla mutane arba'in da biyu, yayin da wasu akalla casa'in suka jikkata.

Ana cikin gyaran ginin ne wanda sama da iyalai dari da hamsin ke zaune a ciki gobarar ta tashi.

Wakilin BBC yace gobarar ta rutsa da mutane da dama yayin da wutar ta kama saman ginin, wanda mesar ruwan kashe gobarar ta kasa isa gunsa.

Baki dayan ginin ya turnike da hayaki kuma wutar ta kama katakan da ake aikin gyaran ginin.