Ana daina artabu a kasar Guinea

Alpha Conde na Guinea Conakry
Image caption Ana ci gaba da artabu a Guinea-Conakry

A kasar Guinea-Conakry an daina artabun da aka kwashe kwanaki biyu ana yi, tsakanin dakarun tsaro da magoya bayan Cellou Dalein Diallo, wanda aka kayar a zaben shugaban kasar na farko, tun bayan da ta samu 'yancin kai.

Sai dai har yanzu ana zaman dar dar, kuma rahotanni sun ce ana tashin hankali a wasu sassan kasar.

Cellou Dalein Diallo yayi kiran da a kwantar da hankali, yana mai cewar, zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Dan takarar da ya lashe zaben, Alpha Conde, ya ce yana son ya shugabanci shirin sasanta 'yan kasar