Saudiyya za ta bi hakkin wata 'yar Indonesia

Shugaban Indonesia, Susilo Bambang Yudhoyono
Image caption Susilo Bambang Yudhoyono

Jami'an Saudiyya sun yi alkawarin cewa, shari'a zata yi aikinta, dangane da lamarin wata 'yar aiki, 'yar kasar Indonesiya, wadda ake zargin cewa, uwayengijin ta sun azabtar da ita.

Wani babban jami'in majalisar Shura ta Saudiyya, Dokta Yehyia Fadel, ya gayawa BBC cewa, galibi akwai kyakyawar hulda tsakanin 'yan kasar Saudiyya da ma'aikatansu na kasashen waje.

Ya ce hukumomin Saudiyya za su gudanar da bincike a kan lamarin, za su kuma ba kowane bangare hakkinsa.

Rahotanni sun ce, 'yar aikin tana can kwance a asibitin Madina, rai kwakwai mutu kwakwai saboda munanan raunukan da ta samu.

Tun farko dai shugaban Indonesia Susilo Bambang Yudhoyono ya yi Allah Waddai da al'ammarin, yana mai kira da a bi ma 'yar aikin hakinta.