Galibin Musulmai sun yi Sallah a yau

Mahajjata a Macca
Image caption Mahajjata a Macca

A yau ne galibin musulmin duniya ke gudanar da bikin sallar layya ko Eid-elkabir wanda shine buki mafi girma da musulmin ke yi a cikin shekara.

Hakan dai ya biyo bayan hawan Arfa da aka yi a jiya Litinin a kasa mai tsarki.

Kimanin mahajjata miliyan ukku ne daga sassa dabam dabam na duniya suke gudanar da aikin hajin a kasar ta Saudiyya.

A lokacin bikin ana bukatar duk musulmin da yake da hali ya yanka dabba a matsayin wata ibada ga ubangiji Allah.

Sai dai a kowace shekara dimbin musulmi ba sa samun damar yin yanka saboda matsin tattalin arziki.