Tarayyar Turai za ta tallafawa Ireland

Image caption Kwamishinan kudi na tarayyar Turai

Tarayyar Turai ta fara shirye-shiryen baiwa gwamnatin Ireland tallafin kudi idan ta bayyana bukatar hakan.

Kwamishinan kudi na tarayyar Turai, Ollie Rehn ne ya bayyana haka a wani taro da ministocin kudi na kasashen Turai su ka yi da jami'an hukumomin hada-hadar kudi na duniya a Brussels game da dimbin basussukan da ake bin Ireland.

Sai dai ministan kudi na Ireland, Brian Lenihan ya ce a shirye kasar ta ke ta biya bashin da kanta.

Yace babu wanda zai so shiga wannan siradi amma dai mun taba ratsa siradin kuma mun ketare lafiya don haka zamu dauki kwararan matakan da ake bukata wurin inganta tsarin bankunanmu domin kare tattalin arzikin Turai baki daya.