Kotu ta kama yan Liberia da satar kayan agaji

Image caption Yan gudun hijira a Liberia

Wata kotu a Amurka ta samu wasu yan Liberia guda biyu da ke aiki a kungiyar agaji ta World Vision da laifin sace fiye da dala miliyan guda daga cikin tallafin da ta baiwa Liberia.

Masu shigar da kara sun ce mutanen biyu, Joe Bondo da Morris Fahnbuleh sun sayar da kusan dukkan abincin tallafin da kungiyar ta baiwa Liberia.

Haka kuma sun sace kayayyakin gini inda suka yi amfani da su wurin ginawa kansu gidaje da dama.

An dai samu mutanen biyu ne da laifin hadin baki, da almundahana, da kuma yin ikirari na karya.