Yan adawar Amurka ce rage makamai sai badi

Image caption Shugaba Obama

Yan jam'iyyar Republican a majalisar dattawan Amurka sun ce ba zai yiwu a amince da yarjejeniyar rage makaman nukiliya tsakanin Amurka da Rasha a bana ba.

Wani fitaccen sanata a jam'iyyar, John Kyl ne ya bayyana haka.

Gaggauta amincewa da dokar na cikin manyan kudirorin gwamnatin shugaba Obama, sai dai sanata Jon Kyl ya ce majalisar dattawa ba za ta iya kammala nazarin dokar da wuri ba.

Wakiliyar BBC ta ce yan jam'iyyar Democrat na ganin yan Republican na son dakile kudirorin shugaba Obama ne bayanda suka samu nasara a zaben rabin wa'adi, amma sun ce masu zabe ba za su so wakilansu su yi sakaci da tsaron kasa ba.