Ban Ki moon na fargabar rikici a Sudan

Image caption Masu zabe a Sudan

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon ya bayyana damuwa game da rahotannin tashin-tashina tsakanin arewaci da kudancin Sudan a wani taro na musamman na kwamitin tsaron majalisar.

Yace musayar munanan maganganu da kuma zargin karya yarjejeniyar tsagaita wuta na iya haddasa rudanin da ka iya hana kuri'ar raba gardamar da za'a yi kan yancin kudancin kasar a Janairu.

Wakiliyar BBC a majalisar dinkin duniya ta ce ana fargabar jinkirta kuri'ar raba gardamar ko kuma kin amincewar arewacin Sudan da a raba kasar na iya bude wani sabon yaki a kasar.

Sai dai wakilan bangarorin biyu sun ce za su amince da sakamakon kuri'ar.