FIFA ta dakatar da Amos Adamu

Amos Adamu da Reynald Tamerii
Image caption Duka mutanen biyu mambobi ne a kwamitin zartarwa na hukumar ta FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta dakatar da Amos Adamu na Najeriya daga harkokin kwallo har tsawon shekaru uku, sannan ta ci tarar sa dala 10,000.

Hukumar ta kuma dakatar da Reynald Temarii na kasar Tahiti tsawon shekara guda, tare da tarar dala 5,000.

Kwamitinta na da'a na FIFA ya same su da laifin yunkuri sayar da kuri'unsu a zaben kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarun 2018 da 2022.

Duka mutanen biyu mambobi ne a kwamitin zartarwa na hukumar ta FIFA.

Hukumar ta kuma wanke Qatar da Portugal - Spaniya daga zargin hada kai domin samun nasara.

Sai a ranar 2 ga watan Disamba ne za a kada kuri'a domin zaben kasashen da za su dauki bakuncin gasar. Dukkanin su dai ba za su kada kuri'a a zaben ba.

'Zan daukaka kara'

Sai dai jim kadan bayan yanke hukuncin, Amos Adamu ya fitar da sanarwa inda ya yi watsi da hukuncin.

Ya ce: "ban ji dadin wannan hukunci da kwamitin da'ar ya yanke ba, na yi imanin cewa za a wanke ni daga zargin,".

"Nan ba da jimawa ba zan daukaka kara game da hukuncin da suka yanke."

Tsofaffin mambobin kwamitin zartarwar hudu - Slim Aloulou na Tunisia da Amadu Diakite na Mali da Ahongalu Fusimalohi na Tonga da Ismael Bhamjee na kasar Botswana - duk sun fuskanci hukunci daga FIFA.

An dakatar da Bhamjee shekaru hudu, Diakite da Fusimalohi shekaru uku-uku, Aloulou shekaru biyu, sannan dukkansu a ka ci tararsu dala 10,000.

Rahoton Sunday Times

A watan Oktoba ne Jaridar Sunday Times, ta wallafa cewar Mr Amos Adamu, wanda ya fito daga Nigeria da kuma Reynold Temarii dan Kasar Tahiti, dukkaninsu sun nuna a shirye su ke su sayar da kuri'un su na zabar kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarun 2018 da 2022.

Jaridar ta ce, Mr Adamu ya bukaci a bashi dala dubu dari takwas don ya gina filayen wasa a Najeriya, da aka tambaye shi yana gani idan a ka bashi kudi don gudanar da aikin kashin kansa hakan za ta sa ya sauya yadda zai kada kuri'a, sai ya ce, ''lallai hakan zai yi tasiri.Tabbas kuwa''.

Ya shaida wa 'yan jaridar cewa shi za a baiwa kudin, ba gwamnatin kasarsa ba.

Ya kara da cewa, yana neman hanyar da zai samu kudi kimanin fan dari biyar don gina filayen wasa.

Jaridar ta ce shi ma Reynald Temarii, wanda shi ne shugaban wata gamammiyar kungiyar kwallon kafa ta yankin Oceania, ya tattauna batun biyan sa kudi don gina wata makarantar koyar da wasanni.

Duka mutanen biyu dai sun musanta rahoton jaridar, suna mai cewa kage a ka yi musu.