Sallar lasar Gishiri a Nijar

Image caption Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun farfado da bikin Sallar lasar gishiri wadda makiyaya a garin Ingall dake Jihar Agadez a arewacin kasar kan yi.

Wannan dai ya biyo bayan dakatar da bikin Sallar da aka yi har na tsawon shekaru uku, sakamakon barkewar rikicin kungiyoyin 'yan tawayen Auzinawa. Albarkacin ajiye makamai da dubban 'yan tawayen suka yi, dubban makiyayan Nijar sun taru a bikin bana, inda makiyaya daga sassa daban- daban na kasar da ma baki su ka taru domin ciyar da dabbobinsu ciyawa da ruwan gishiri.

Wannan bikin dai na baiwa 'yan yankin wata damar cudanya, tare kuma da habaka kasuwanci har ma da raya a'ladu.

Duk da dai cewa bikin na bana ya zo ne daidai lokacin da wasu 'yan ta'adda suka sace wasu turawa biyar 'yan kasar Faransa da kuma wasu 'yan Afrika biyu dake aikin hakar ma'adinai a kamfanin AREVA a garin Arlit, hukumomi a garin na Ingall sun ce bikin ya yi armashi` .