Ingila ta sha kashi a hannun Faransa

England
Image caption Fabio Capello ya kyale Gerrard a wasan ya dade duk da cewa yana fama da rauni

Faransa ta yi tattaki har birnin London inda ta doke Ingila da ci biyu da daya, a wasan sada zumuntar da suka buga a filin wasa na Wembley.

Kareem Benzema ne ya zira kwallon farko a minti na 16, yayinda Valbuena ya kara ta biyu a minti na 55.

Sai a minti na 86 ne sannan Peter Crouch ya zirawa Ingila kwallo dayan da ta ci.

Wakilin BBC na fannin wasanni ya ce wannan wasa ya nuna cewa akwai babban kalubale a gaban Ingila, ganin yadda Faransa ta yi kaca-kaca da su.