Kotu ta samu tsararren Guantanamo da laifi

Image caption Ahmad Khalfan Ghailani

Wata kotun farar hula a Amurka, ta kama mutum na farko daga cikin wadanda aka tsare su a sansanin Guantanamo Bay, da laifin hada bakin wajen amfani da wani makami mai fashewa da ya lahanta dukiyar Amurka.

An zargi Ahmed Khalfan Ghailani, dan kasar Tanzania, wanda aka gurfanar gaban kotun da hannu a hare-haren bama-baman da aka kai ofisoshin jakadancin Amurka da ke Kenya da Tanzania, wadanda suka kashe kimanin mutane dari biyu da ashirin da hudu.

Sai dai kotun wadda ke birnin New York ta wanke shi daga sauran daruruwan tuhume-tuhumen da ake yi masa, na aikata kisa da ta'addanci.

Kotun ta yi watsi da mafi yawan hujjojin da aka gabatar mata kasancewar hukumar leken asiri ta CIA ce ta tattara bayyanan ta hanyar azabtarwa.