Yiwuwar kai harin ta'addanci a Jamus ta karu

Jirgin saman Air Berlin
Image caption Jirgin saman Air Berlin

Hukumar 'yan sandan yaki da miyagun laifufuka ta Jamus ta ce, an gano wani kunshi a cikin wata jaka, yayin da ake loda ta cikin wani jirgin sama, wanda aka shirya zai tashi daga Namibia zuwa birnin Munich na kasar ta Jamus, a jiya Laraba.

Wata na'ura mai binciken kwakwaf ta gano cewa, kunshin na dauke da wata na'urar tayar da bam da aka jona da wani agogo, amma ba a san ko akwai wasu nakiyoyi a wurin ba.

Daga karshe jirgin ya sauka lami lafiya a birnin na Munich.

Wasu bayyanan sirri sun nuna cewa, akwai wani shiri na kai hari a kasar ta Jamus nan da karshen wannan wata na Nuwamba.