Sojin Najeriya sun ceto mutane 19 a Naija Delta

Image caption Mayakan Naija Delta

A Najeriya, rundunar sojin kasar ta ce ta ceto mutane goma sha tara ciki har da 'yan kasashen waje guda bakwai a wani hari da ta kai kan wasu sansanonin guda biyu na 'yan bindigar Naija Delta a jiya Laraba.

Jami'an tsaro a Najeriya dai sun ce an kai samamen ne ta ruwa, da ta sama, da kuma kasa.

Wannan harin ya kasance wata sabuwar dabara ta aikin soja a yankin.

Sannan kuma shi ne aikin ceto na farko da aka yi nasara ba tare da an kashe kowa ba.