Kotu ta hana belin Henry Okah a Afirka ta Kudu

Henry Okah
Image caption Henry Okah

Wata kotu a Afirka ta kudu ta ki bada belin dan Najeriyar nan da ake zargi da shirya kai hare haren bam, wadanda suka janyo hallakar mutane 12 a Abuja, a ranar daya ga watan Oktoban da ya wuce, a lokacin da Najeriyar ke bikin cika shekaru 50 da samun 'yan cin kai daga turawan mulkin mallakar Birtaniya. Alkalin kotun ya ce, Henry Okah shi ne tsohon shugaban kungiyar MEND, ta masu ikirarin kwato hakkokin yankin Niger Delta mai arzikin mai na Najeriya.

Kungiyar MEND ce ta dauki alhakin hare haren da aka kai a Abujar.

Henry Okah ya ce ba hannunsa a kai hare haren, kuma a yanzu ba shine shugaban kungiyar MEND ba.

Kwana daya bayan hare haren na Abuja ne aka kama shi a gidansa da ke birnin Johannesburg.