Ana farautar Fulani a Guinea Conakry -ICG

Masu zabe a kasar Guinea
Image caption Masu zabe a kasar Guinea

Kungiyar International Crisis Group (ICG) mai fafutukar hana tashe-tashen hankula a duniya ta ce jami'an tsaron kasar Guinea sun kai hare-hare a kan magoya bayan dan takarar shugabancin kasar da ya sha kaye, wanda ya fito daga daya daga cikin manyan kabilun kasar guda biyu, Cellou Dalein Diallo.

Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa irin wannan hari ka iya kaiwa ga fito-na-fito a tsakanin kabilun kasar.

Kungiyar ta International Crisis Group ta ce al'amura sun rincabe a kasar ta Guinea sakamakon tsundumar da sojoji suka yi cikin tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar.

Kungiyar, mai hedkwata a birnin Brussels, ta ce sojojin kasar masu sanye da jajayen huluna, wadanda dama sun yi kaurin suna wajen keta hakkin bil Adama, suna bi suna zakulo 'yan kasuwa Fulani a babban birnin kasar, Conakry.

Kungiyar ta ce tun bayan barkewar rikici lokacin da aka bayyana sakamakon zaben ranar Litinin, an kashe akalla mutane goma sha-biyu a birnin na Conakry.

Akasarin magoya bayan dan takarar da ya sha kayen dai Fulani ne kuma kungiyar ta ce jami'an tsaro na kai hari a kansu a sauran sassan kasar.

Sai dai babban hafsan sojojin kasar, Janar Nouhou Thiam, ya yi watsi da wadannan zarge-zarge, yana mai cewa a ko da yaushe sojoji na ba da kariya ga al'ummar kasar da dukiyoyinsu.

A cewarsa, duk wanda ya ce sojojin kasar na keta hakkin bil Adama sai ya kawo hujjarsa ta fadar hakan.