An kwato yarinyar da aka sace a Bauchi

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Bauchi a Najeriya sun nuna cewa jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da yarinyar nan 'yar shekara goma sha daya wadda wasu mutane suka sace a farkon wannan watan.

Jami’an dai sun bayyana gano yarinyar ne jiya da dare, sun kuma ce sun kama wadansu mutane da ake zargi da sace ta da kuma muggan makamai.

Jami’an sun ce sun yi nasarar hakan ne sakamakon wani aikin hadin gwiwar jami’an tsaro na farin kaya, wato SSS, da 'yan sanda, da kuma sojoji.

Mahaifin yarinyar, Alhaji Ahmad Almustapha—wanda tsohon shugaban Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi ta Najeriya ne—ya shaidawa BBC cewa yarinyar mai suna Jamila ta koma gida cikin koshin lafiya.

Matsalar satar mutane ana garkuwa da su dai ta zama tamkar ruwan dare gama duniya a Nijeriya.