Mahakar kwal ta rutsa da mutane 27.

'Yan sanda a New Zealand sun ce har yanzu ba a tantance ba, game da lokacin da ma'aikatan ceto zasu iya shiga cikin wata mahakar ma'adinai, inda har yanzu ba a ji duriyar wasu ma'aikatan ma'adinan ba, su ashirin da bakwai, bayan fashewar wasu nakiyoyi.

Sun ce katsewar wutar lantarki na shafar aikin na'urorin shaskar iska a mahakar kwal din dake kudancin kasar.

Dangin ma'aikatan ma'adinan dai sun shafe dare ne a kusa da ramin hakar ma'adinan, inda ma'aikatan ceto ke kokarin kwantar masu da hankali.