Rami ya rufta da masu hakar ma'adinai 27 a New Zealand

Wurin hakar ma'adinin Pike River a New Zealand
Image caption Wurin hakar ma'adinin Pike River a New Zealand

A tsibirin sashen kudu na kasar New Zealand, an kafa wata cibiyar bada gajin gaggawa ga iyalan wasu mahaka ma'adinan da aka rutsa da su, a wani ramin hakar ma'adinan da ya rufta, bayan fashewar nakiyoyi a karkashin kasa.

Mahaka ma'adinai 27 ne ba aji duriyarsu ba bayan fashewar nakiyoyin.

Biyu daga cikin mahakan ma'adinan sun tsira da ransu, inda suka samu fitowa daga ramin na Pike River Coal.

Yanzu haka 'yan uwa da abokan arziki na can cikin tararradi, inda zasu shafe daren yau, suna zaman jiran tsammani na samun labarin halin da suke ciki.