Kotu ta rusa kwamatin PDP na Filato

Okwesilieze Nwodo, shugaban jam'iyar PDP
Image caption Kotu ta rushe kwamatin da PDP ta nada a Filato

Kotun daukaka kara dake zamanta a birnin Jos na jihar Filaton Najeriya ta rusa kwamatin rikon da jam'iyar PDP mai mulkin kasar ta nada a jihar.

Jam’iyar PDPn ta rabe gida biyu ne, inda gwamnan jihar Jonah Jang ke jagorantar bangare guda, sannan daya bangaren ke samun jagorancin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Ibrahim Mantu da kuma tsofofin gwamnonin jihar, Joshua Dariye da Fidelis Tapgun.

Kuma hakan ya sanya helkwatar jam'iyar dake Abuja ta nada kwamatin riko; sai dai bangaren da gwamna Jang ke marawa baya ya kai jam'iyar kara babbar kotu, kuma kotun ta baiwa bangaren gwamna nasara.

Sai dai jam'iyar bata gamsu ba , inda ta tafi kotun daukaka kara;ita kuma kotun ta yanke wannan hukunci.