NATO za ta kirkiri garkuwa a Turai

Shugabannin kungiyar NATO
Image caption Shugabannin kungiyar NATO

Shugaba Obama na Amurka ya bayar da sanarwar cewa kasashen kungiyar tsaro ta NATO sun amince su kirkiro wani sabon shiri na kariya daga harin makami mai linzami a Turai.

Yayinda yake jawabi a wurin taron kolin kungiyar kawancen ta NATO, Shugaba Obama ya yaba da yarjejeniyar a matsayin martani ga abin da ya kira barazana ta zamani.

“A karo na farko mun amince mu kirkiro wani mataki wanda zai ba daukacin kasashen Turai da ke kungiyar NATO, da Amurka, da al'ummominsu kariya daga harin makami mai linzami.

“Wannan muhimmin mataki ci gaba ne a kan sabon tsarin kariya daga harin makami mai linazmi na Amurka da na sanar bara.

“Wannan wata katanga ce ga dukkan kawayenmu daga barazana ta zamani; ta kuma nuna irin dogewarmu wajen kare al'ummomin kasashenmu daga barazanar hari da makami mai linzami”, inji Obama.

Shugaba Obama ya kuma ce za a shigar da Rasha cikin shirin saboda, a cewarsa, ita ma tana fuskantar irin barazanar da kasashen kungiyar ta NATO ke fuskanta.

Rasha dai na kallon wannan shiri a matsayin zagon kasa ga harkar tsaronta—fargabar da kungiyar ta NATO ke fatan kawarwa ta hanyar shigar da kasar ta Rasha cikin shirin.