Amurka ta dage haramcin kai agaji Sudan

Rumfar kada kuri'ar raba gardama
Image caption Rumfar kada kuri'ar raba gardama a Sudan

Amurka ta dage haramcin da ta sanya na kai kayayyakin agaji zuwa kasar Sudan don bayar da damar aikewa da na'u'orori masu kwakwalwa gabannin zaben raba gardama a kan kudancin Sudan da zai kai ga raba kasar gida biyu.

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da umurnin cewa a dage haramcin da aka sanya a kan tallafin da Amurka ke baiwa kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasar ta Sudan.

A wata takarda daga Fadar Shugaban kasa, Mista Obama ya ce an yi la'akari ne da muradun kasar wajen bayar da damar ci gaba da aikewa da kayayyakin.

An dai yanke shawarar gudanar da zaben rabe gardamar ne a watan Janairu mai zuwa, bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya wanda ya kawo karshen yakin basasa a kasar shekaru biyar da suka gabata.