An soke zaben 'yan takara goma a Afghanistan

Afghanistan
Image caption Afghanistan

Hukumar sauraren kararrakin zaben da Majalisar Dinkin Duniya ke mara wa baya a Afghanistan ta soke zaben 'yan takara goma sha tara da suka lashe zaben majalisar dokoki a watan Satumba. Hukumar ta ce an soke zaben ne, domin galibin kuri'un da suka samu na magudi ne.

Wakilin BBC a Afghanistan ya ce an sha yin gangami a Kabul da sauran biranen kasar, ana kiran a soke hukumar zaben. 'Yan takara da dama sun yi korafin cewa wasu abokan hamayarsu masu daurin gindi sun rika murde kuri'unsu.

Su dai 'yan takarar da aka soke zabensu ba su da ikon daukaka kara.