Jam'iyyar CDS Rahama zata zabi dan takarar shugaban kasa

Tutar jamhuriyar Nijer
Image caption Tutar jamhuriyar Nijer

A jamhuriyar Niger an bude wani zama na musamman na uwar jam'iyyar CDS -RAHAMA ta tsohon shugaban kasar, Alhaji Mahammane Ousmane.

A lokacin taron ne ake sa ran za a kaddamar da dan takarar shugaban kasa na zaben da za a gudanar karshen watan janairun shekara mai zuwa.

To sai dai bisa dukkan alamu ana samun wata takaddama, game da tsayar da Alhaji Muhaman Usman kan wannan mukami, sakamakon yadda Alh Abdu Labo, mataimakin shugaban jam'iyyar ta CDS Rahama ke adawa da hakan.