Falasdinawa :Babu tattaunawa sai Isra'ila ta daina gina matsugunai

Jagoran Falasdinawa, Mahmud Abbas ya kawar da yuwuwar komawa shawarwarin sulhu da Isra'ila sai fa idan sun dakatar da gina gidajen da suke yi a dukkan yankunan da suka mamaye, ciki har da Gabashin Birnin Kudus.

Ya ce, mun jaddadawa Amurkawa cewa babu ruwanmu da tayin da suke kokarin yi wa Isra'ila. Dangantakarsu da Isra'ila daban.

Mahmud Abbas na maida martanin ne kan rahotannin da ke cewa Amurka ta yi wa Isra'ila tayin agaji ta fuskar ayyukan soja da kuma diflomasiyya, domin ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa a gabar yammacin kogin Jordan kawai.

A cikin watan Satumba ne aka koma shawarwarin sulhu tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, amma aka dakatar bayan 'yan makonni, bayan da Isra'ila ta ki ta kara wa'adin dakatar da gina matsugunan Yahudawa.