Sarki Abdalla na Saudiyya zai je Amruka neman magani

Sarki Abdullah na Saudiyya
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Sarki Abdulllah na Saudiyya na shirin zuwa Amurka domin neman magani, a sakamakon ciwon bayan da yake fama da shi. A gobe Litinin, idan Allah Ya kai mu ne ake sa ran Sarkin mai shekaru tamanin da shida, zai tafi Amurkar, kwanaki uku bayan an kwantar da shi a wani asibiti a Saudiyya.

Yarima mai jiran gado, Sultan bin Abdul-Aziz, wanda shi kuma shekarunsa tamanin da biyar, yana murmurewa ne daga maganin da aka yi masa na cutar daji a kasar waje.

An ce yana kan hanyar komawa gida Saudiyya domin rike ragamar mulki, kafin komawar yayansa.