Nasarorin taron kolin kungiyar NATO

Shugabannin kungiyar NATO
Image caption Shugaba Medvedev na Rasha da wasu shugabannin kungiyar NATO

Shugabannin kungiyar kawance ta NATO sun kammala taron kolin da suka gudanar a birnin Lisbon na kasar Portugal tare da cimma wasu muhimman yarjejeniyoyi.

To ko wadanne irin nasarori ne taron ya yi?

Taron kolin dai ya gudana cikin lumana; an kuma yi ittifaki a kan yanayin kawancen na NATO a karni na ashirin da daya.

An kuma amince da rage kashe kudade a wasu bangarori don samar da kariya ga mambobin kungiyar daga sabbin barazana, musamman ma ta intanet.

Haka nan kuma kasashen sun amince da shirin samar da kariya daga harin makami mai linzami.

Babu shakka da sauran aiki a gaba, to amma kungiyar ta NATO ta kafa tarihi da ta shigar da Rasha cikin tsarin na bayar da kariya ga mambobinta.

Yaukaka dantanka da Rasha dai na cikin muhimman nasarorin da taron ya yi.

Dangane da batun Afghanistan kuwa, kungiyar ta amince da kawo karshen aikin sojinta da danka al'amuran tsaro a hannun mutanen Afghanistan din a shekarar 2014—amma fad a sharadin idan yanayin tsaro ya inganta.