Redknapp : Tottenham za ta iya lashe gasar Premier

Redknapp
Image caption Tottenham ta taka rawa sosai a bara

Kociyan Tottenham Harry Redknapp ya ce kungiyar shi za ta iya lashe gasar Premier bayanda suka doke Arsenal da ci 3-2.

Sai da Arsenal ta zira kwallaye biyu sannan daga bisani Tottenham ta rama, abinda ya ba ta damar samun nasara irin wannan a karon farko tun 1993.

"Ya kamata mu nemi daukar kofi," a cewar kociyan bayanda 'yan wasansa suka zira kwallaye uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a filin wasa na Emirates.

Ya kara da cewa: "za mu iya doke kowa,." Wannan nasara ta kara dawo da mu sahun wadanda za su iya daukar kofi.

"Idan 'yan wasana suka yarda da kansu kamar yadda na yarda da su, to za mu iya cimma burinmu".

Rabon da Tottenham ta dauki League dai tun shekarar 1961.