Dalilin rashin zartar da dokoki a Majlisar Wakilai

Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dimeji Bankole
Image caption Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dimeji Bankole

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ce rashin zartar da dokoki masu yawa ba alama ce ta gazawar mambobinta ba, illa dai suna yin dokoki kalilan ne wadanda za su yi tasiri.

Rahotanni dai na cewa a cikin kudurorin doka kusan dari biyar da aka gabatar a gaban Majalisar daga shekarar 2007 zuwa watan Oktoban da ya gabata, 'yan majalisar sun zartar da dokoki 140 ne kawai.

Sai dai mataimakin shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Majalisar Wakilan, Honourable Shu'aibu Hashimu Abdullahi, ya ce Majalisar ta taka rawar-gani wajen yin dokoki masu inganci.

“Ayyukan ne suka yi yawa a gaban Majalisa: wadanda ba a zartar da su ba su kusan dari uku din nan, ana cikin aiki ne a kansu a kwamitoci daban daban na Majlisa—wadansu kwamitocin sun gama rahoto a kai sun gabatar a zauren Majalisa, sai dai Majalisa ba ta kai ga duba rahotanninsu domin zartarwa ba.

“Wadansu [kwamitocin] kuma sun ji ra’ayin ’yan Najeriya, ba su kammala rubuta rahotanninsu su gabatar a gaban Majalisa ba...shi yasa yawan ya kai haka”.