Jean Pierre Bemba ya gurfana a gaban kotun duniya

Jean Pierre Bemba
Image caption Ana zargin Mr Bemba da aikta laifuffukan yaki

Wani tsohon mataimakin shugaban kasar jamhuriyar Demakrdiyyar Congo, Jean Pierre Bemba, ya gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dake Hague.

Mr Bemba na fuskantar aikata laifukan yakin da dakarun 'yan tawayensa suka aikata kan fafaren hula a makwabciyar kasar, watau Jumhuriyar Afrika ta Tsakiya a shekara ta 2002 da 2003.

Masu shigar da kara suka ce ba abinda Mr Bemba yai domin hana mutanansa yiwa jama'a da dama fyade.

Sai dai kuma daya daga cikin lauyoyin Mr Bemba ya ce sam bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba.