Jam'iyyar Green Party ta nemi a gudanar da zabe a Ireland

Ireland
Image caption Shugabannin Ireland suna bayyana amincewarsu da bashin Tarayyar Turai

Jami'iyyar Green Party ta gamayyar gwamnatin hadin guiwar Ireland ta yi kira da a gudanar da sabon zabe a watan Janairu, bayanda Tarayyar Turai ta baiwa kasar rance.

Jam'iyyar ta ce jama'ar Ireland na bukatar "tabbaci ta fuskar siyasa".

A ranar Lahadi ne gwamnatin kasar ta amince da karbar rancen Euro biliyan 90 daga Tarayyar Turai, kuma za ta bayyana tsarin kasafin kudi na shekaru hudu ranar Laraba.

Sai dai Firayim Ministan kasar ta Ireland, Brian Cowen, ya ce za a daidaita a kan wasu batutuwan da suka shafi rancen a tattaunawar da za a yi tsakanin kasar da Tarayyar Turai da kuma Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) a 'yan makwanni masu zuwa.

Za a yi amfani da rancen ne, don cike gibin kasafin kudin kasar da kuma karawa bankunan kasar karfi.

Kudin dai zai fito ne daga kafofi daban-daban na Tarayyar Turai da kuma asusun IMF, kuma zai zo da ka'idoji.

'Mai kunci ga jama'ar Ireland'

Tana kuma fuskantar zaben cike gurbi a ranar Alhamis, wanda ka iya rage rinjayen da ta ke da shi na kujeru uku.

Jagoran jam'iyyar Green Party John Gormley, wanda shi ne ministan muhalli, ya ce yana bukatar a gudanar da zaben, a tsakiyar watan Janairu.

Jam'iyyar ta ce za a gudanar da zaben ne kawai bayan an gabatar da kuma amincewa da tsarin kasafin kudin shekara ta 2011.

"Barin kas, ba tare da gwamnati ba, a irin wannan hali na rashin tabbas zai iya zamowa da illa sosai, kuma zai sabawa alhakin da ke kanmu na jama'a," a wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar.

Mista Gormley ya ce makon da ya gabata ya kasance mai kunci ga jama'ar Ireland. "Mutane na jin an ci amanarsu".

Ya kara da cewa Pira Minista Brian Cowen ya nuna rashin jin dadinsa a kan hukuncin da jam'iyyar ta Green ta yanke.

Ka'idoji

Sakamakon wannan bashi, za a bukaci kasar ta Ireland ta aiwatar da wasu manufofi da za su samar da daidaito a harkar banki da kuma kasafin kudi na gwamnati.

Tuni Firayim Minista Cowen ya bayar da sanarwar daukar tsauraran matakan karfafa tattalin arzikin kasar tare da rage gibin kasafin kudin da dala biliyan ashirin nan da shekara ta 2015.

Wannan taimako ya nuna burin da Tarayyar Turai ke da shi na tabbatar da daidaito a tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na Euro da ma kasashen Tarayyar baki daya.

Kasar da za a mayar da hanakali a kanta nan gaba kuma ita ce Portugal, wadda ita ma gwamnatinta ke fama da wawakeken gibin kasafin kudi.

Ministocin kudi na Tarayyar Turai dai na fatan ta hanyar taimakawa Ireland za su hana matsalar yaduwa.