Tarayyar Turai ta amince ta ba Ireland rance

Ministan kudi na Ireland, Brian Lenihan
Image caption Ministan kudi na Ireland, Brian Lenihan

Tarayyar Turai ta amince ta samar da rancen da zai taimakawa kasar Ireland ta magance matsalolin tattalin arzikin da ta ke fuskanta.

Sai dai Firayim Ministan kasar ta Ireland, Brian Cowen, ya ce za a daidaita a kan wasu batutuwan da suka shafi rancen a tattaunawar da za a yi tsakanin kasar da Tarayyar Turai da kuma Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) a 'yan makwanni masu zuwa.

Za a yi amfani da rancen ne, wanda watakila zai haura dala biliyan dubu dari, don cike gibin kasafin kudin kasar da kuma karawa bankunan kasar karfi.

Kudin dai zai fito ne daga kafofi daban-daban na Tarayyar Turai da kuma asusun IMF, kuma zai zo da ka'idoji.

Za a bukaci kasar ta Ireland ta aiwatar da wasu manufofi da za su samar da daidaito a harkar banki da kuma kasafin kudi na gwamnati.

Tuni Firayim Minista Cowen ya bayar da sanarwar daukar tsauraran matakan karfafa tattalin arzikin kasar tare da rage gibin kasafin kudin da dala biliyan ashirin nan da shekara ta 2015.

Wannan taimako ya nuna burin da Tarayyar Turai ke da shi na tabbatar da daidaito a tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na Euro da ma kasashen Tarayyar baki daya.

Kasar da za a mayar da hanakali a kanta nan gaba kuma ita ce Portugal, wadda ita ma gwamnatinta ke fama da wawakeken gibin kasafin kudi.

Ministocin kudi na Tarayyar Turai dai na fatan ta hanyar taimakawa Ireland za su hana matsalar yaduwa.

Karin bayani