Zaman zulumi a garin Langtang na jahar Plateau

Jahar Plateau a taswirar Najeriya
Image caption Jahar Plateau a taswirar Najeriya

Ana zaman dar-dar a yankin Langtang na jihar Filaton Nijeriya, sakamakon wata hatsaniya da aka yi a cikin garin na Langtang.

Tashin hankalin ya barke ne bayan da aka yi ta baza jita-jita, kan cewa akwai wasu mutane masu satar al'aura a garin.

Lamarin ya cusa fargaba a zukatan mazauna garin, inda kuma matasa suka kama wasu mutane da suke zargi da aikata wannan lamari, kana suka lakada masu duka, kafin jami'an tsaro su shawo kan lamarin.

Wasu rahotanni sun ce an sami hasarar rayuka.

Rundunar 'yan sandan jihar Filaton ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin.