Kungiyar RATTAWU ta fara yajin aiki a Nijeriya

Wasu ma'aikatan gidan rediyo
Image caption Wasu ma'aikatan gidan rediyo

Ma'aikatan gidajen rediyo da 'yan jaridu a Najeriya karkashin kungiyar RATTAWU ta ma'aikatan gidajen rediyo da wasan kwaikwayo, tare da kungiyar 'yan jaridu ta kasa NUJ sun tsunduma cikin wani yajin aiki na gargadi a yau.

Kungiyoyin biyu na kokawa ne a bisa binda suka kira dan kankanin albashi da gwamnati ke biyansu idan aka kwatanta da wahalhalun aiki da rayuwa da suke fama da su.

A baya dai gidajen rediyo da talabijin na gwamnatin tarayyar kasar ne za su yi wannnan yajin aiki na kwanaki 3 na gargadi, to amma bayanai na nuna cewa har ma gidajen rediyo da talabijin na jihohi sun shiga wannan yaji.