Atiku ya ce zai iya kada Shugaba Jonathan

Image caption Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria Atiku Abubakar, ya ce yana da kwarin gwiwar kada shugaba Goodluck Jonatahan a zaben fidda gwani na takarar shugabancin kasar a jamiyyar PDP mai mulki.

A karon farko da yake maida martani tun bayan zabar sa da aka yi a matsayin dan takarar da ya fito daga arewacin kasar a karsahin jamiyyar PDP, tsohon mataikakin shugaban kasar ya kuma jinjinawa sauran 'yan takarar ukku wadanda ba su yi nasara ba.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru a Abuja wanda ya samu halatar shugabannin yakin neman zaben sauran 'yan takarar da kuma wasu magoya bayansu.